LABARAN DUNIYA

Tuesday, September 12, 2023

Hukumomin Najeriya sun kama bama-bamai 399 da miyagun ƙwayoyiHukumomin Najeriya sun kama bama-bamai 399 da miyagun ƙwayoyi

 NDLEA



11 Satumba 2023

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA sun ce sun kama bama-bamai kimanin 399 daga hannun wani mutum a kan hanyar Mokwa-Jebba a ranar 7 ga watan Satumba.


Hukumar ta ce ta damƙa mutumin da ake zargi mai shekara 39 ga hukumomin soji a jihar da abin ya faru wato Neja.


Ya dai bayyana cewa an miƙa masa bama-baman ne a wani dandali da ke cikin birnin Ibadan, domin kai wa wani mutum a jihar Kaduna.


Zuwa yanzu babu masaniya a kan abin da za a yi da bama-bamai masu tarin yawa haka da mutumin ya yi safara zuwa arewacin Najeriya.


TALLA


Bama-baman dai irin waɗanda ake haɗawa a gida ne, da aka fi sani da suna abubuwa masu fashewa.


Jihar Kaduna da maƙwabtanta irinsu Neja da Zamfara da Katsina, suna fama da mummunan rikicin 'yan fashin daji masu kai hare-hare da bindigogi a kan ƙauyuka da garuruwa.


Mayaƙan waɗanda akasari kan auka wa mutane a kan babura, sun yi ƙaurin suna wajen kashe-kashe da jikkata fararen hula, da satar mutane ciki har da mata da ɗalibai 'yan makaranta, inda suke tsare su har sai an biya kuɗin fansa.


A watan Maris ɗin 2022, hukumomi sun zargi 'yan fashin dajin da haɗa kai da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram - ta 'yan ta-da-ƙayar-baya musamman a arewa maso gabas - da ƙaddamar da hari kan jirgin ƙasan da ke cikin gudu a hanyarsa ta Abuja zuwa Kaduna.


Maharan sun yi amfani da bama-bamai wajen tarwatsa wani sashe na titin jirgin ƙasa da taragwansa, don tilasta wa jirgin tsayawa tare da sace gomman fasinjoji, bayan sun kashe wasu tare da raunata wasu da dama.


A baya-bayan nan ma, wani rahoto da aka kwarmata a kafofin yaɗa labarai, ya ambato hukumar tsaron farin kaya ta DSS na gargaɗin hukumomi da cewa wasu mutane ne kitsa makamancin harin da aka kai a kan jirgin ƙasa.


Sai dai, baya ga hare-haren 'yan fashin daji, jihar Kaduna ta yi ƙaurin suna kan rikicin ƙabilanci da na addini da ma rikicin manoma da makiyaya

Saturday, September 9, 2023

RIBAR HAKURI

 Mahakurci mawadaci duk wadda zayi hakuri a rayuwa zai samu babban rabo . 

WATAN RABIYUL-AUWAL